Isa ga babban shafi

Amurka ta maido da 'yan kasarta sama da 20 daga sansanin adana mutane na IS dake Syria

Amurka ta sanar da karbar wasu turawa sama da 20 daga sansanin da mayakan IS ke tsare mutane, wanda ke arewa maso gabashin Syria, inda suke tsare da dubban mutane.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden REUTERS - Tom Brenner
Talla

Bayanai sun ce rabin adadin mutanen da Amurka ta mayar  gida ‚yan asalin kasar ne.

Wannan shi ne karbar turawa daga hannun IS da Amurka ta taba yi a tarihi, lamarin da ke zuwa bayan da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi gargadin cewa wannan aiki zai iya zuwa da tangarda.

Da yake bayani a shafin sa na X sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya ce cikin mutane da aka amso 11 ‚yan asalin Amurka ne, wadanda suka hadar da kananan yara biyar, sai kuma wani matashi guda.

Sauran sun hadar da shida ‘yan asalin kasar Canada da kuma hudu ‘yan Jamus sai daya dan asalin kasar Finland, kuma 8 daga cikin wannan adadi kananan yara ne.

Da yake karin haske mai magana da yawun hukumar tsaron sirri ta Amurka Mattew Miller ya ce har yanzu akwai sauran Amurkawa 25 a irin wadannan guraren adana jama’a.

Dama Amurka ta jima tana kiraye-kiraye ga kasashen turawa da su hada kai wajen karbo ‘yan kasar su dake irin wadannan sansanonin adana mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.