Isa ga babban shafi
Yakin Rasha da Ukraine

Ya zama dole Putin ya bar karagar mulki - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce babu yadda za’ayi takwaransa na Rasha Vladimir Putin ya ci gaba da zama a karagar mulki sakamakon mamayar da ya yiwa Ukraine, yayin da ya bayyana mamayar a matsayin shirin kasar da ya kasa haifar da ‘da mai ido.

Hotunan shugabannin kasashen Amurka da Rasha, Joe Biden da Vladmir Putin
Hotunan shugabannin kasashen Amurka da Rasha, Joe Biden da Vladmir Putin AFP - ERIC BARADAT,PAVEL GOLOVKIN
Talla

Biden wanda yake jawabi a birnin Warsaw ya danganta jajircewar kasar Ukraine dangane da mamayar Rasha ta kai musu kamar bijirewa mulkin Tarayyar Soviet lokacin neman ‘yanci, yayin da ya bayyana cewar ya dace duniya ta shirya fuskantar rikici na dogon lokaci nan gaba.

Shugaba Biden ya bayyanawa mutane Ukraine cewar duniya na tare da su, yayin da ya shaidawa mutanen Rasha cewar ba sune abokan gabar su, saboda haka su zargi shugaba Putin saboda takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kakaba musu.

Shugaban Amurkar ya kuma gargadi Putin da kar ya kuskura yace zai mamaye koda taki guda na wata kasa dake cikin kungiyar NATO, domin kuwa zai gamu da martini mai karfi daga kasashen dake cikin kawancen.

Biden ya bayyana fatar samun makomai mai kyau da haske nan gaba wanda zai samu ginshikin dimokiradiya da kudirorin ta, yayin da yake jaddada bukatar kawar da Putin daga karabar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.