Isa ga babban shafi

Hungary ta ki amincewa da yunkurin zaman Ukraine mamba a EU

Firaministan Hungary Viktor Orban ya nanata kiransa ga kungiyar Tarayyar Turai wajen ganin ba ta bijiro da tattaunawar mayar da Ukraine mamba a kungiyar yayin babban taronta da ke tafe ba, taron da zai gudana a wani yanayi da Kiev ke halin tsaka mai wuya sakamakon yankewar tallafin da kasashe ke bata a yakinta da Rasha.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine lokacin da ya ke sauraren jawabin shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen a zauren Majalisar Kungiyar da ke Brussels.
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine lokacin da ya ke sauraren jawabin shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen a zauren Majalisar Kungiyar da ke Brussels. AFP - HANDOUT
Talla

Dukkanin shugabannin kasashen EU in banda Orban sun aminta da tattaunawa don bai wa Ukraine damar zama mamba a cikin kungiyar wanda aka tsara gudanar da wani zama na sirri tsakanin kasar da mambobi 26 a wani gefe na taron da zai fara gudana yanzu haka a birnin Brussels don karkare batun.

Firaminista Orban wanda shi ne ya kange tallafin yuro biliyan 50 da EU ke shirin bai wa Ukraine daga kasafin kudin kungiyar, duk da cewa alamu na nuna a wannan karon ya goyi bayan dadadden tallafin da EU ke bai wa Kiev amma ba daga kasafin kudin kungiyar ba, lura da tsaka mai wuyar da kasar ke ciki sakamakon gaza samun tallafi daga kawayenta kasashen yammaci a yakin na kusan shekaru 2 da ta ke gwabzawa da Rasha.

Bisa ka’ida sai dukkanin mambobin EU sun aminta da kudirin shigar da Ukraine cikin kungiyar ne za ta iya samun wannan dama, sai dai tirjiyar ta Orban na zuwa a wani yanayi da Kiev ta samu kanta a tsaka mai wuya bayan gaza samun tallafin dala biliyan 60 da Amurka ta shirya bata saboda yadda Majalisa ta ki amincewa.

A cewar Viktor Orban bayan isar shi birnin Brussels, ‘yan Hungary basa biyayya ga matsin lamba, kalaman da kai tsaye ke matsayin shagube ga shugabannin na EU, ya na mai cewa za su tirje kan matsayarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.