Isa ga babban shafi

Zelensky ya tabbatar da kisan Sojin Ukraine dubu 31 a yakin Rasha

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce Sojin kasar dubu 31 suka mutu a yakin shekaru 2 da suka shafe suna gwabzawa da Rasha, a kokarin baiwa kasar kariya daga mamayar makiya.

Volodymyr Zelensky na Ukraine.
Volodymyr Zelensky na Ukraine. AP - Evgeniy Maloletka
Talla

Zelensky a jawabin da ya gabatar wajen taron zauren shekara na Kyiv ya ce dukkanin wadanda suka mutu rayukansu basu tafi a banza ba, domin kuwa sun sadaukar da rayukansu ne domin kasarsu kuma domin cikakken ‘yancin al’ummarsu.

A cewar Zelensky baya ga sojojin akwai kuma dubun-dubatar fararen hula da suka mutu wadanda ba za a iya kaiwa ga tantance adadinsu ba har sai zuwa bayan kawo karshen yakin.

Wannan dai ne karon farko da Kyiv ke sanar da adadin sojojinta da suka mutu a fagen daga tun bayan faro yakin a ranar 24 ga watan Fabarairun 2022.

A bangaren Rasha ta bakin kafar labaran Mediazona mai zaman kanta ta ce akalla mutane dubu 75 suka mutu a 2022 da 2023 da kaso mai yawa da dakarun sa kai wadanda bad aga cikin sojin kasar ba.

Sai dai sashen leken asiri na Amurka ya ce daga faro yakin zuwa watan Disamban bara akwai sojojin Rasha dubu 315 da ko dai suka mutu ko kuma suka jikkata a yakin na Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.