Isa ga babban shafi

Faransa ta kiyasta cewa dakarun Rasha dubu 150 ne suka mutu a Ukraine

Faransa ta yi ƙiyasin cewa dakarun Rasha aƙalla dubu 100 da 50 ne suka mutu a yaƙin da ake gwabzawa a Ukraine, a cewar ministan harkokin wajen ƙasar, Stephane Sejourne a yayin wata ganawa da aka wallafa a wata jaridar ƙasar Rasha a wannan Juma’a.

Ministan harkokin wajen Faransa, Stephane Sejourne.
Ministan harkokin wajen Faransa, Stephane Sejourne. © Ken Ishi / via Reuters
Talla

Da ya ke amsa tambayoyi daga wakilin jaridar  Novaya Gazeta Europe, Sejourne ya ce Faransa ta yi kiyasin cewa waɗanda wannan  yaƙi da yake shiga shekara ta 3 yanzu ya rutsa da su ta wajen rasa rai da rauni sun kai dubu dari 5.

Sejourne wanda ya ce faduwar Rasha na nan tafe, ya ce yammacin nahiyar Turai za ta ci gaba da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya har sai ta ga abin da ya ture wa buzu naɗi.

A watan Fabarairu, shugaban Ukraine,Volodymyr Zelensky  ya ce dakarun Rasha dubu 100 da 80 ne suka mutu a wannan yaƙi, a yayin da Birtaniya ta yi ƙiyasin cewa sojojin Rasha da suka mutu ko suka jikkata sun kai dubu dari 4 da 50.

A watan Afrilu, kafar yaɗa labaran BBC ruwaito cewa sama da dakarun Rasha dubu 50 ne suka mutu a yaƙin, tana mai nuni da bayanai daga wakilanta, da kuma wasu kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.

Yaƙin Ukraine ya ɓarke ne ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2022, bayan da shugaban Rasha, Vladimir Putin ya sanar mamaya a kan Ukraine, lamarin da ya rikiɗe zuwa mummunan yaƙi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.