Isa ga babban shafi

Ina da tabbacin Rasha za ta yi nasara a yakin da ta ke a Ukraine- Kim Jong Un

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya ce Rasha na samun gagarumar nasara a fadan da ta ke yi da makiya, kalaman da ke zuwa a ziyarar da shugaban ke ci gaba da gudanarwa a Moscow, a wani yunkurin samar da kyakkyawar alaka ciki har da ta aikin soji tsakanin kasashen biyu. 

Ganawar Putin da Kim.
Ganawar Putin da Kim. via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Duk da cewa kawo yanzu babu wasu bayanai da ke tabbatar da cewa akwai wata yarjejeniya da ke bai wa Rasha damar samun makamai da kuma kayan aikin soji daga Korea ta Arewa, amma Amurka ta yi zargin cewa akwai yiyuwar kasar na shirin taimaka wa Moscow a yakin da ta ke yi da Ukraine. 

Bayan isarshi a Rasha cikin jirgin kasar mai sulke, Shugaba Kim Jong Un ya yi musabaha da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a garin Vostotchny da ke matsayin babbar cibiyar harba tauraron dan adam a gabashin kasar Rasha. 

Shugabannin biyu sun tattauna har tsawo sa’o’i biyu, kafin daga bisani a shriya wa shugaban na Koriya ta Arewa wata gagarumar liyafar cin abincin rana. 

Kim Jong Un ya ce ya na da yakinin cewa sojoji da kuma al’ummar Rasha, za su yi nasara a yakin da su ke yi da wadanda ya kira su a matsayin masu nuna dagawa a wannan zamani.

Haka zalika, Kim ya kuma yi jinjina ta musamman ga sojojin Rasha saboda irin jarumtakar da su ke nunawa a fafatawar da suke yi da kasar ta Ukraine. 

Wannan ne dai karo na farko da shugabannin biyu suka yi ganawa da juna tun bayan ganawarsu ta 2019, yayin da Amurka ke nuna fargabar cewa Korea ta Arewa za ta iya samar wa Rasha da muggan makamai don yakar Ukraine. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.