Isa ga babban shafi

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sunayen wadanda ake zargi da kisan Delta

Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta fidda sunayen mutane 8 da take nema ruwa a jallo, wadanda ake zargi da kashe sojojin kasar 17 a yankin Okuama da ke Jihar Delta.

Hotunan mutane 8 da rundunar sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo, bayan da aka zargesu da kashe sojoji 17 a jihar Delta.
Hotunan mutane 8 da rundunar sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo, bayan da aka zargesu da kashe sojoji 17 a jihar Delta. © Daily Trust
Talla

A lokacin da daraktan yada labaranta Manjo Janar Edward Buba ke ganawa da manema labarai a shalkwatar tsaron kasar da ke Abuja da safiyar Alhamis din nan, ya ce akwai tukwicin da za a bada ga duk wanda ya bada masaniyar inda wadanda ake zargin suke.

Daga cikin wadanda rundunar ta ayyana take nema sun hada da Farfesa Ekpekpo Arthur da Reuben Baru da Akata Malawa David da Andaowei Dennis Bakriri da Akevwru Daniel Omotegbo da Sinclear Oliki da Clement Ikolo Ogenerukeywe sai kuma wata mata Mrs Igoli Ebi.

Janar Buba ya bukaci masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma musamman da ke yankin Niger Delta, su taimaka wa rundunar wajen gano inda wadanda ake zargin suke.

Idan ba a manta ba a ranar 14 ga wannan watan ne dai, wasu matasa suka yi wa jami’an sojojin Najeriya da ke aiki a karkashin bataliya ta 181 kawanya, a lokacin da suka je aikin wanzar da zaman lafiya a Okuama, sannan suka yi musu kisan gilla.

Gawarwakin sojojin Najeriya 17 da aka yi wa kisan gilla a yankin Niger Delta.
Gawarwakin sojojin Najeriya 17 da aka yi wa kisan gilla a yankin Niger Delta. © Daily Trust

A jiya Laraba ne kuma aka gudanar da jana’izarsu a babbar makabartar kasar da ke Abuja, inda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu halarta.

Shugaba Tinubu ya kaarrama sojojin da aka yi wa kisan gillar

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da bai wa sojojin da aka yi wa kisan gilla  lambar girmamawa ta kasa da kuma alkawarin gina wa kowanne guda daga cikinsu gida a inda suke so tare da bai wa 'yayansu tallafin karatu har zuwa matakin jami'a.

Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin gudanar da jana'izar soji ga wadannan sojoji 17, inda ya bada umarnin cewar hukumomin soji su tabbatar da cewar an biya hakkokin wadannan soji nan da kwanaki 90.

Nigerian service chiefs
Nigerian service chiefs © Daily Trust

Tinubu ya bayyana cewar shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya masa bayani a kan irin gagarumar gudumawar da Laftanar Kanar Ali, kwamandan sojin da aka kashe ya bayar wajen yaki da Boko Haram da kuma 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma, kafin mayar da shi yankin Neja Delta.

Sojojin da aka kashe sun shiga cikin kundin tarihi

Shugaban ya ce a madadin Najeriya yana mika sakon jinjina ga Kanar Ali saboda yadda ya ci gaba da bada gagarumar gudumawa a rundunar sojin har zuwa lokacin da aka masa kisan gillar, yayin da shi da jami'ansa suka shiga cikin tarihi a matsayin gwarazan da suka bada gudummawa sosai.

Tinubu ya ce a matsayinsa na babban kwamandan sojin Najeriya baki daya, yana sane da irin gagarumar gudumawar da bajintar da sojojin suka bayar wajen tabbatar da tsaron Najeriya, inda yake cewa ba za a taba mantawa da su ba.

Shugaban ya ce duniya na sane da rawar da sojojin Najeriya ke takawa a Afirka da kuma wasu sassan duniya, saboda haka ba za su bar iyalansu su taggayara ba.

Jana'izar ta samu halartar manyan hafsoshin tsaro da ministoci da 'iyalan sojin da suka rasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.