Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya na da kwarewar da za su kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya - Kwankwaso

Tsohon Ministan Tsaro, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce sojoji za su iya kawo karshen matsalar tsaron da ya addabi ƙasar.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yayin da yake jawabi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yayin da yake jawabi Premium Times
Talla

Jagoran jami’yyar NNPP na kasa, ya bayyana haka ne yayin wata  zantawa da ya yi da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin zartarwa na jami’yyar a Abuja.

Tsohon ministan Ya ce duk da cewa haƙƙin Gwamnatin Tarayya ne, ta magance matsalar tsaro, amma ’yan Najeriya na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bai wa hukumomin tsaro muhimman bayanai.

Kwankwaso ya kuma kara da cewa “A matsayina na tsohon ministan tsaro kuma tsohon babban jami’in tsaro na Jihar Kano na tsawon shekara takwas, wanda ya yi gwagwarmayar siyasa, a yi imanin tukarar ƙalubalen tsaro na hannun gwamnatin tarayya.

Kwankwaso ya kara da cewa:

 

Kowa na ganin yadda jihohi ke ƙirƙiro jami’an tsaro. Wani lokaci abun ya ba ka dariya. A halin da ake ciki a Najeriya sojoji ne kaɗai za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaro. sannan ya ce dole ne kowa ya ba da haɗin kai don ganin an samu zaman lafiya a wannan ƙasar tamu.

Wasu daga cikinmu da ke kauyuka suna ganin yadda mutanenmu suke zuwa gonaki. Yanzu kuma ba sa iya zuwa gona. Ana korar su daga ƙauyuka da garuruwansu. Masu laifi da ’yan bindiga na sace ’ya’yanmu kullum,  in ji shi.

 

Kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya ce jam’iyyarsa tana da tsarin da za ta bi wajen magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

Ya ce, jam’iyyar NNPP ita ce kawai mafita ga ’yan Najeriya, inda ya ce jam’iyyar APC da PDP sun gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.