Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta yi karin albashi ga rukunnan ma'aikatun kasar 6

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da karin albashin tsakanin kashi 25 da 35 ga wasu rukunnai 6 na ma’aikatun kasar da ke karkashin tsarin albashin bai daya, a wani yunkuri na sassauta musu radadin tsadar rayuwar da al’ummar kasar ke fama da ita.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

A yammacin jiya Talata ne kakakin hukumar kula albashin ma’aikata ta Najeriyar NSIWC Emmauel Njoki ya sanar da matakin yayin wani jawabinsa a Abuja fadar gwamnatin kasar wanda ya ce zai shafi bangarori 6 na sassa da ma’aikatun da ke karkashin gwamnatin tarayya gwamnati.

Sai dai wannan kari kai tsaye bai shafi tattaunawar da yanzu haka ake yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago na kasar ba, wadanda suka bukaci karin albashi ga ma’aikata tun bayan matakin cire tallafin man fetur a watan Mayun bara.

Kamar yadda Mr Emmanuel ya bayyana sabon karin albashin ya fara aiki tun daga ranar 1 ga watan Janairu karin albashin zai fara aiki, haka zalika karin ya shafi hatta ‘yan fansho wadanda aka yi musu karin da ya fara daga kashi 20 zuwa 28 duk dai a kokarin kawo sauki ga matsin rayuwar.

Har yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC wadanda ke son gwamnati ta kara yawan mafi karancin albashi a kasar zuwa dubu 615 daga dubu 30 da ake bayarwa a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.