Isa ga babban shafi
'YAKI DA TA'ADDANCI

Amurka tace sojojin Rasha sun kutsa kai sansaninta dake Nijar

NIJAR – Kasar Amurka ta sanar da cewar sojojin Rasha sun kutsa kai cikin sansanin sojin saman Nijar wanda ke dauke da sojojin ta, bayan umarnin da gwamnatin kasar ta bayar na ficewar su daga cikin ta.

Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Chiani. 16/09/23
Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Chiani. 16/09/23 © Presidence du Niger
Talla

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bai wa Amurka umarnin janye sojojin kusan dubu guda dake cikin kasar, bayan kwashe shekaru suna hadin gwuiwa wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel wadanda suka yi sanadiyar hallaka dubban mutane.

Wani jami'in sojin Amurka ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar wadannan sojoji na Rasha basa cudanya da na su, sai dai sun mamaye wani sashe na sansanin sojin saman mai lamba 101, wanda ke kusa da tashar jiragen saman Diori Hammani a birnin Yammai.

Sakatren tsaron Amurka, Lloyd Austin
Sakatren tsaron Amurka, Lloyd Austin © Maya Alleruzzo / AP

Wannan yunkuri na sojojin Rasha ya tabbatar da kusancin su da sojojin Amurka a dai dai lokacin da kasashen biyu ke matukar takun saka a bangaren soji da kuma diflomasiya dangane da yakin Ukraine.

Wannan mataki kuma ya dada jefa shakku a kan makomar kayayyakin sojin da Amurka ta kashe miliyoyin daloli wajen kafa su a cikin kasar, yayin da jami'in sojin ya bayyana halin da suke ciki a matsayin na 'dan gajeren lokaci wanda zasu iya jurewa.

Sakataren Tsaron Amurka Austin Lloyd dake tsokaci a kan lamarin ya yi watsi da duk wata fargabar samun arangama a tsakanin sojojin kasashen biyu dake Nijar da kuma makaman da suka mallaka, yayin da ya bayyana cewar dakarun Rashar na wani bangare ne na daban wanda baya kusa da kayan sojin Amurkar.

Lloyd yace yana matukar mayar da hankali a kan kare sojojin Amurka da kuma kayan aikin su, yayin da ya tabbatar da cewar basa fuskantar wata barazana a Nijar.

Sojojin da suka kwace mulki a wasu kasashen Afirka sun bai wa Amurka da kawayen ta umarnin janye dakarun su a wani yunkuri na nesanta kan su daga gwamnatocin kasashen yammacin duniya.

Bayan shirin janyewa daga Nijar, sojojin Amurkar sun kuma fice daga Chadi a 'yan kwanakin da suka gabata, yayin da su ma na Faransa suka janye daga kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.