Isa ga babban shafi
Kasuwanci

Dambarwar EFCC da wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin Najeriya kan badakalar kudi

Wallafawa ranar:

Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matakin hukumar da ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annti EFCC na kaddamar na farautar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da kuma binciken wasu tsoffin mukarraban gwamnatin da ta shude kan cin hanci da rasha da kuma rufta da ci da dukiyar al’umma.

Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. © EFCC
Talla

A Najeriya, cikin ‘yan makonnin baya-bayan nan kusan za’a iya cewa hankulan al’ummar ƙasar sun karkata ne kan matakan da hukumar EFCC ke dauka kan wasu tsaffin jjiga-jigan gwamnatin da ta gabata, inda hukumar ta tsare kuma take shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman ƙasar ƙarkashin tsohon shugaban ƙasa Mohammdu Buhari, wato Hadi Sirika, bisa zargin almundahana na ƙudi da suka kai sama da naira biliyan takwas.

Yayin da a bangare guda, aka shiga wasan buya da cece-kuce tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello da ke cewa abi umurnin kotu kan shirin kamashi yayinda shugaban hukumar ta EFCC ke cewa tabbas zai yi murabus muddun tsohon gwamnan bai gurfana don amsan laifin almundahanan sama da naira biliyan tamanin ba.

Wadannan da wasu batutuwa da suka shafi tattalin arzikin Najeriya na kunshe a cikin wannan shiri, ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.