Isa ga babban shafi

Tarayyar Turai za ta kara azama wajen samar wa Ukraine makamai

Tarayyar Turai ta sha alwashin ci gaba kara azama  wajen  kera harsashe da alburusai da sauran makamai a wannan shekarar a matsayin martini ga bukatar hakan da Ukraine ta mika mata ta neman dauki a yakin da take gwabzawa da Rasha.

Shelkwatar Tarayyar Turai da ke birnin Brussels na kasar Belgium.
Shelkwatar Tarayyar Turai da ke birnin Brussels na kasar Belgium. AP - Virginia Mayo
Talla

A yayin ziyarar da ya kai kasar Estonia, jami’in kasuwanci cikin gida na Tarayyar Turai, Thierry Breton ya ce a wannan shekarar, Turai za ta samar da harsashe guda miliyan 1 da dubu dari 3.

 

A karshen wannan makon Ukraine, ta bakin ministan harkokin wajenta, Dmytro Kuleba ta nuna matukar bukatar neman karin harshasai da sauran makamai, kana ta bukaci Turai ta taka wa Rasha birki wajen samun makamai daga yankin.

 

Kuleba ya ce wasu alkalumma sun nuna cewa, kashi 95 na mahimman makaman Rasha da aka samu a Ukraine an kera su ne a kasashen yammacin Turai.

 

Sai dai Kuleba bai yi karin bayani a game da sahihancin ikirarin nasa ba, amma a kowane Ukraine tana warware duk wani makami mai linzami da jirgi mara matuki da aka kai mata hakri da su don tantance asalinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.