Isa ga babban shafi

Ana daf da sake fafatawa tsakanin Biden da Trump a zaben shugaban Amurka na 2024

Shugaban Amurka, Joe Biden da abokin Hamaayyarsa,, kuma tsohon shugaba, Donald Trump sun lashe zaben fid da gwani a jiohi da dama a kuri’ar da aka kada a jiya Talata, lamarin da ke nuni da cewa za su fafata da juna a zaben watan Nuwamba, kuma ya ke kara matsin lamba a kan abokiyar hamayyar tsohon shugaban, Nikki Haley ta hakura da takara a jam’iyyar Republican.

Shugaba Joe Biden da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaba Joe Biden da tsohon shugaban Amurka Donald Trump. AP
Talla

Nasarorin wadannan manyan ‘yan siyasa biyu a manyan jihohin kasar da suka hada da jihohin California da Texas masu yawan wakilai, na nuni da yadda fafatawar neman shugabancin kasar za ta kasance.

Nikki Haley ta lashe jihar Vermont, inda ta taka wa Trump birki wajen lashe dukkannin jihohin, amma tsohon shugaban kasar ya lashe sauran jihohin da ake ganin za su cire mata kitse a wuta, kamar su Virginia, Massachusetts da Maine, wadanda suke da adadi mai   yawa na masu zabe da ke da sassaucin ra’ayi.

A daya bangaren kuwa, fafatawa daya tilo da Biden ya yi rashin nasara a Talata ita ce a Samoa, wani karamin yanki na Amurka a yammacin tekun Pacific, inda wani dan takara da ba a sani sosai ba, Jason Palmer ya doke shi da kuri’u 51 da 40.

Nan gaba a wannan wata ne karin jihohi za su gudanar da zabukansu, inda sakamakonsu za su tabbatar da Trump da Biden a matsayin ‘yan takaran jam’iyyunsu.

Amma sakamakon kuriar da aka kada a wannan rana ta Talata, ya sa ana ganin tabbas Biden da Trump za su sake fafatawa a babban zaben watan Nuwamba. Biden mai shekaru 81 da Trump mai 77 ne dai suke kan gaba a jam’iyyunsu, duk kuwa da korafin cewa sun tsufa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.