Isa ga babban shafi

Blinken na ziyara a Saudiya da nufin kawo karshen hare-haren Isra'ila kan Gaza

Sakatare harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Saudi Arabia tun a cikin daren jiya Laraba, don tattaunawa da mahukuntan kasar da ke matsayin jagora tsakanin kasashen Larabawa a kokarin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin Gaza.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken bayan isa birnin Jedda na Saudi Arabia a kokarin tattaunawa da mahukuntan kasar kan yakin Isra'ila a Gaza.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken bayan isa birnin Jedda na Saudi Arabia a kokarin tattaunawa da mahukuntan kasar kan yakin Isra'ila a Gaza. © Evelyn Hockstein, Reuters
Talla

Blinken wanda wannan ne karo na 6 da ya ke kai ziyara gabas ta tsakiya tun bayan faro luguden wutar Isra’ilan kan al’ummar yankin Gaza, da zuwa yanzu ya hallaka kusan mutum dubu 32 tare da raba wasu miliyan 1 da dubu 500 da muhallansu, bayanai sun ce bayan kammala tattaunawa a Saudi Arabia zai kuma yada zango a Masar inda zai tattaunawa da wasu jagororin yankin na Falasdinu a birnin Alqahira.

Tuni dai sakataren harkokin wajen na Amurka ya samu tarba daga Yarima Faisal bin Farhan sakataren wajen Saudiyan a Riyadh yayinda kowanne lokaci daga yanzu ake tsammanin Blinken ya samu ganawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyar Muhammad bin Salman.

Bayanai sun ce yayin tattaunawar Yarima Faisal bin Farhan da Antony Blinken sakataren wajen na Saudiya ya jaddadawa Amurka bukatar da ke akwai na ganin Isra’ila ta kare rayukan fararen hula.

Ziyarar ta Blinken na zuwa ne a wani yanayi da yunwa ke ci gaba da kisan tarin kananan yara a yankin na Gaza ciki har da sabbin haihuwa a dai dai lokacin da al’ummar Musulmi ke azumin watan Ramadana a bangare guda Isra’ila ke zafafa hare-hare hatta akan masallata inda cikin kasa da sa’o’i 24 ta hallaka mutane fiye da 100 daga jiya zuwa yau.

Duk da cewa batun samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ya fi daukar hankali a tattaunawar amma wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na reuters cewa yayin zaman na yau Alhamis, shugabannin na Larabawa za su gabatarwa Amurka wani kunshin kudiri da suke ganin zai kawo karshen rikicin na tsawon shekaru tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Sai dai babban batun da zaman zai fi mayar da hankali kamar yadda AFP ya ruwaito shi ne sakin fursunonin bangarorin biyu da ke tsare a hannun kowannensu wato bangaren Isra’ilan da kuma Hamas.

Zaman tattaunawar ta birnin Alqahira dai zai samu wakilcin masu shiga tsakanin daga Qatar da na Masar kana na Amurka da kuma bangaren shugabancin Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.