Isa ga babban shafi

Blinken ya koma Gabas ta Tsakiya don neman tsagaita wuta a Gaza

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya fara wata ziyara a Gabas ta Tsakiya a wannan Laraba, a wani sabon yunƙuri na laluɓo wata yarejejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake tsakanin Isra’ila da Hamas.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. via REUTERS - POOL
Talla

Biyo bayan gazawa da aka yi ƙoƙarin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza a farkon watan azumi na Ramadan a makon da ya gabata, an fara wani sabon zaman tattauna batun kawo ƙarshen wannan yaƙi a Qatar.

Sai dai a halin da ake ciki, babu wata alama ta dakatar da wannan yaƙi da ya tagayyara ilahirin yankin Zirin Gaza tare da tilasta wa ɗaruruwan dubban Falasdinawa arcewa don neman mafaka a kudancin yankin da aka mamaye.

Kusan watanni 6 da fara wannan yaƙi, Amurka, wadda ita ce babba a cikin masu goyon bayan Isra’ila ta sha yin kira ga ƙawartata ta bari a shigar da ƙarin kayayyakin jinƙai  cikin Gaza, duba da irin halin tagayyara da ake ciki a yankin.

Blinken zai kasance a kasar Saudi Arabia a wannan Laraba, kuma a Alhamis zai ziyarci Masar wadda ke makwaftaka da Gaza, kuma ke cikin jerin tattaunawa da aka yi don sasanta wannan rikici a baya.

Tun da farko a wannan mako, Blinken ya yi gargaɗin cewa a halin da ake ciki kowa na cikin matsalar matsananciyar yunwa, kuma ya zama dole a dauki matakin kawo sauƙi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.