Isa ga babban shafi

Iran ta gargadi Isra'ila kan shirinta na mamaye Zirin Gaza

Iran ta gargadi Isra’ila da cewar muddin ta kuskura ta mamaye Zirin Gaza, to fa tamkar ta bude kofofin da wasu bangarori ko kasashen yakin Gabas ta Tsakiya za su shiga yakinta da Hamas, ta hanyar marawa Falasdinawan baya.

Wasu daga cikin tankokin yakin Isra'ila akan iyakarta da Zirin Gaza.
Wasu daga cikin tankokin yakin Isra'ila akan iyakarta da Zirin Gaza. REUTERS - VIOLETA SANTOS MOURA
Talla

Ministan harkokin wajen Iran Hossien Amir-Abdollahian yayi wannan gargadi ne a yayin da dubban sojojin Isra’ila da suka hallara akan iyakarsu da Zirin Gaza, ke jiran a basu  umarnin kadddamar da farmaki ta kasa da zummar murkushe kungiyar Hamas.

A halin yanzu, mutane fiye da dubu 2 da 670 ne suka mutu, dubu daya daga cikinsu kananan yara, wasu mutanen kusan dubu 10 kuma suka jikkata, yayin hare-haren ramuwar gayyan da Isra’ila ke kai wa ta sama a Zirin Gaza, tun bayan farmakin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban nan.

A nata bangaren gwamnatin Isra’ila ta ce akalla mutane dubu 1 da 400, cikinsu har da sojoji 289, da kuma wasu ‘yan kasashen waje, mayakan Hamas suka kashe a tsawon mako gudan da aka shafe.

Duk da cewar Amurka na ci gaba da nanata goyon baya ga Isra’ila a yakin da take da Hamas, a ranar Lahadi, shugaba Joe Biden ya bayyana shirin dakarun Isra’ilar na sake mamaye Zirin Gaza a matsayin babban kuskure, domin kungiyar Hamas ba ta wakiltar baki dayan Falasdinawa, ko da yake ya jaddada cewar murkushe mayakan abu ne da ake bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.