Isa ga babban shafi

Amurka da Isra'ila za su nazarci tayin yarjejeniyar da Hamas ta amince da shi

Hamas ta ce ta amince da tayin yarjejeniyar tsagaita wutar da Masar da Qatar suka miƙa mata a Litinin da zummar kawo ƙarshen yakin da aka shafe watanni kusan 7 ana yi, amma ma’ikatar  harkokin wajen Amurka  ta ce tana nazari kai.

Wani ɓangare na birnin Rafah da hare-haren Isra'ila suka lalata.
Wani ɓangare na birnin Rafah da hare-haren Isra'ila suka lalata. AP - Fatima Shbair
Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Mathew Miller  ya ce lallai Amurka ta karɓi martanin Hamas a game da yarjejeniyar, sai dai babu wani ƙarin bayani da zai yi a game da haka, yana mai jaddada cewa cimma yarjejeniya zai gyara dukkannin ɓangarorin da ke rikici da juna.

Rahotannin sun ce masu shiga tsakani a wannan tattaunawar sun miƙa wa Isra’ila martanin Hamas jim kaɗan bayan amincewa da tayin yarjejeniyar, kuma gwamnatin Isra’ilar na nazari a kansa, sai dai ofishin fira minista Benjamin Netanyahu ya ƙi yin tsokaci a kai.

Wata majiyar diflomasiyya da ke da masaniya a kan tattaunawar ta ce bayan ganawa mai tsawo tsakanin daraktan ƙungiyar leƙen asiri na Amurka CIA, Bill Burns da fira ministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a birnin Doha, masu shiga tsakanin sun shawo kan Hamas ta amince da yarjejeniyar mai rukunnai uku.

 Yarjejeniyar da Hamas ta amince da  ita ta kunshi matakai uku, wanda za a shafe kwanaki 42 a kowanne mataki, kuma zai soma ne da janyewar  Isra’ila a da’irar  Netzarim, wadda Iisra’ila ke amfani da ita wajen raba arewaci da kudancin Gaza.

Abubuwan da yarjejeniyar  ta ƙunsa

Majiyoyi sun ce tayin yarjejeniyar daga Masar da Qatar , wadda Hamas ta amince da shi tana da matakai 3, inda  kowanne 3, inda kowanne zai dauki kwanaki 42.

 

Za a fara da rukuni na farko, inda Isra’ila za ta janye daga da’irar Netzarim, wadda Isra’ila ke amfani da shi wajen rana arewacin Gaza da Kudanci.

 

Rukuni na biyu zai ƙunshi amincewa dakatar da aikin da sojoji ke yi, tareda janyewar dakarun Isra’ila gaba daya daga Zirin Gaza.

 

Rukuni na 3 na yarjejeniyar ya kuma ƙunshi amincewa da kawo ƙarshen ƙawanyar da Isra’ila ta wa Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.