Isa ga babban shafi

UNICEF ta ce ƙananan yara dubu 600 na fuskantar ƙarin bala'i a Rafah

Asusun kula da ƙanana yara na duniya, UNICEF ya yi gargdin cewa yara dubu dari 6 da ke jibge a birnin Rafah na zirin Gaza na fuskantar ƙarin matsanancin bala’i, tana mai nuna rashin amincewarta da umurnin ficewa daga yankin da Isra’ila ta bayar gabanin harin da ta yi barazanar kaiwa.

Wasu ƙanan yaraan Gaza dayaƙi ya ɗaiɗaita.
Wasu ƙanan yaraan Gaza dayaƙi ya ɗaiɗaita. © Mohammed Dahman / AP
Talla

A wata sanarawa, UNICEF ta ce lura da cinkoson yara a wannan birni na Rafah,  da kuma hare-haren Isra’ila da ke illa ga fararen hula da kuma mahimman ababen more rayuwa  bai kamata a tilasta wa al’umma barin yankin a wannan yanayi ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa al’umar Gaza sun daɗe da fadawa cikin mawuyacin hali, inda daga cikin mutane miliyan 1 da dubu dari 2 da ke neman mafaka a Rafah, kimannin dubu ɗari 6 yara ƙanana ne, waɗanda aka ɗaiɗaita sau da  dama, kuma ba su da wurin zuwa.

Daraktar Asusun Kula da Ƙananan yaran, Catherine Russell ta ce sama da kwanaki 200 da aka shafe ana yaƙi a Gaza ya yi mummunan tasiri a rayuwar ƙanana yaran.

Ta ce yanzu Rafah ya zama birni na ƙananan yara, waɗanda ba su da wani wuri mara haɗari da za su samu mafaka a Gaza, tana mai gargadin cewa harin sojin ƙasa da  Isra’ila ke shirin kai wa Rafah  zai kawo ruɗani da tashin hankali kuma a lokacin da yaran suka riga suka galaibaita a jiki da kuma tunaninsu.

UNICEF ta yi ƙiyasin cewa yawan al’ummar Rafah ya ninka har sau 5 idan aka kwatanta da yadda mazauna birnin suke dubu dari 2 da 50 kafin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.