Isa ga babban shafi

Amurka ta dakatar da kudurin kai jirgi makare da bama-bamai zuwa Isra'ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da Shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon da ya gabata, sakamakon rashin bin umurninta na kaucewa kai hare hare a birnin Rafah dake kudancin Gaza. 

El primer ministro israelí, Benjamín Netanyahu y el secretario de Estado de Estados Unidos, Antony Blinken. en The Kirya, que alberga el Ministerio de Defensa israelí, después de su reunión en Tel Aviv el 12 de octubre de 2023.
El primer ministro israelí, Benjamín Netanyahu y el secretario de Estado de Estados Unidos, Antony Blinken. en The Kirya, que alberga el Ministerio de Defensa israelí, después de su reunión en Tel Aviv el 12 de octubre de 2023. AFP - JACQUELYN MARTIN
Talla

Sakatare janar na Majalisar dinkin duniya Antoni Guterese ya ce babban kuskure ne mamayar da israila ta kai Rafah, la’akari da cewa an kasa amfani da hanyoyin da aka saba bi wajen isar da kayakin agaji, haka ma tuni aka rufe hanyoyi 2 mafi sauki da a ke bi dan shigar da kayayyaki cikin Gaza .

A jiya Talata ne majiyoyin suka bayyana cewa bangarorin da ke rikici da juna sun amince da komawa kan teburin sulhu, domin tattauna batun tsagaita wuta tare da kawo karshe yakin na Israila da Hamas.

Rundunar sojin Israila ta ce tun da sanyin safiyar ranar Talata ne dakarunta suka kwace ikon kan iyakar mashigin Rafah bayan hare haren sama da su ka shafe tsawon lokaci suna yi, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 27.

Ita ma Hukumar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce a kowace rana ta Allah Falasdinawa da dama na fuskantar barazanar rasa rayukansu saboda hana kayayyakin agaji shiga inda suke da Israila ta yi.

Akalla Falasdinawa 34,789 ne sojojin Israila suka kashe tun bayan barkewar yaki a cikin watan oktoban da ya gabata, yayin da wasu dubu 78,204 suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.