Isa ga babban shafi

Wasu kasashen Turai da Amurka sun sha alwashin taimakawa Isra'ila

Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Italiya da kuma Amurka sun fidda sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi Allah wadai da harin da kungiyar Hamas ta kai Isra’ila, tare da yin alkawarin taimakawa kasar wajen kare kanta. 

Wasu sojojin Isra'ila
Wasu sojojin Isra'ila REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

 

Sanarwar dai ta biyo bayan ganawar da Firaministan Burtaniya Rishi Sunak da shugaban Amurka Joe Biden da Emmanuel Macron na Faransa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da kuma Firaministar Italiya Giorgia Meloni suka yi ne ta wayar tarho. 

Kasashen sun bayyana rashin jin dadinsu kan harin da Hamas ta kai Isra’ila, wanda suka bayyana a matsayin na ta’addanci, musamman yadda suka ce kungiyar ta kashe mutanen da basuji basu gani ba tare da kame wasu da ta yi. 

Goyon bayan Isra'ila

Shugabannin sun ce kasashensu za su marawa Isra'ila baya a kokarinta na kare kanta da al'ummarta daga irin wannan ta'asa na Hamas. 

Sanarwar ta kara da cewa kasashe biyar sun amince da halalcin muradun al'ummar Falasdinawa, kuma suna goyon bayan daidaiton adalci na cin gashin kai tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, sai dai sun ce ko kadan Hamas ba ta bayar da gudunmar da ta dace ga al'ummar Falasdinawa, face ta’addanci da zubar da jini da ta yi. 

Ci gaba da hada kai da Isra'ila

Shugabannin kasashen sun ce cikin kwanaki masu zuwa, za su ci gaba da hada kai a matsayinsu na aminan Isra'ila, don tabbatar da cewa ta iya kare kanta, da kuma shimfida sharuddan samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. 

A ranar Abasar din da ta gabata ne dai, kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila wanda ya yi sanadiyar mutane sama da dari 9 daga bangaren Isra’ila tare da raunata wasu sama da dubu daya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.