Isa ga babban shafi

Isra'ila ta zafafa hare-hare a yamma da kogin Jordan

Yayin da Isra’ila ke ci gaba da ruwan wuta Gaza a kokarin da ta ke yi na shafe Hamas daga doron kasa, bayanai na nuna cewa Sojojin kasar sun yi wani atisaye da ke nuna suna gab da kutsa kai Gaza ta kasa.

Ruwan wuta ne da Isra'ila bata taba yin makamancin sa a yamma da kogin Jordan ba
Ruwan wuta ne da Isra'ila bata taba yin makamancin sa a yamma da kogin Jordan ba AP - Adel Hana
Talla

Bayanai na nuna cewa cikin sa’o’i 24 Tel-Aviv ta zafafa hare-hare a yamma da kogin Jordan abinda ba’a ga irin sa ba tun bayan fara yakin makonni uku da suka gabata.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka kasa cimma matsaya kan hanyoyin da za’a bi wajen kawo karshen rikicin bangarorin biyu, karo na biyu a majalisar dinkin duniya, bayan da Rasha da China suka ki amincewa da shawarar Amurka na dakatar da shigar da kayan agaji Gaza da kuma baiwa mayakan Hamas makamai.

Amurka dai na bukatar a dakatar da shigar da kayayyakin agaji yankin na Gaza, amma bata bada shawarar hana ayyukan jin kai ba, shawarar da Rasha da China suka ce bata yi kusa da hankali ba.

Sai dai kuma bayan wannan taro da aka tashi baram-baram kungiyar tarayyar turai ta sanar da dakatar da shigar da kayan agaji Gaza, abinda ya yi dai-dai da shawarar da Amurkan ta bayar, to amma tuni wasu kasashen turai suka ki amincewa da wannan yunkuri.

A wani abu mai kama da sauyawar alkiblar yakin, China ta sanar da aike da wasu manyan jiragen yaki guda shida zuwa gabas ta tsakiya, kwanaki uku bayan da Amurka ta tura nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.