Isa ga babban shafi

Amurka ta kai hare-hare kan sansanonin soji 2 na Iran a Syria

Sakataren Tsaron Amurka, Lloyd Austin ya ce sojin kasar ta  kai hare-hare kan wasu sansanoni biyu da rundunar Juyin- Juye Halin Musulunci na Iran ke amfani da su tare da kungiyoyin da ke da nasaba da  ita a daren Alhamis, lamarin da ke zuwa a yayin da Isra’ila ke ci gaba da tsananta hare-harenta  a yankin Gaza.

Sakataren Tsaron Amurka, Lloyd Austin.
Sakataren Tsaron Amurka, Lloyd Austin. AP - Matthias Schrader
Talla

A wata sanarwa da ya fitar, Sakataren Tsaron an Amurka, Lloyd Austin ya ce matakin da rundunar sojiin kasar ta dauka, martani ne ga jerin hare-haren da kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran suka fara kai wa dakarunta tun daga ranar 17 ga wannan wata na Oktoba.

Fadar gwamnatin Amurka ta fada a wata a sanarwa cewa sai da ta aike da sako ga shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei  a game da hare-haren da ake kai wa dakarun kasar a Gabas Ta Tsakiya a daidai lokacin da Isra’ila da Hamas ke gwabza fada.

Sai dai Amurka ta ce wannan mataki da ta dauka  a  kan Iran da kungiyoyin da take mara wa baya a Syria ba shi da nasaba da Isra’ila, hasali ma ba ta tuntubi Isra’ilar ba kafin daukar sa.

A waje  daya kuma, Isra’ila ta ci gaba da yin ruwan wuta a Gaza a daren Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a, inda ta lalata gine-gine da ke kunshe da gidajen jama’a, lamarin da ya  yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama galibin su kananan yara.

Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta wallafa sunayen dubban mutanen da suka mutu a yankin, a matsayin martani ga kalaman shugaban Amurka Joe Biden na nuna kokwanto a kan adadin wadanda Isra’’ila ta kashe

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.