An kama hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a rikicin Gaza
Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh ya ce, suna gab da cimma matsaya kan sulhu," a wani sako da ya wallafa a kafar sadarwa ta Telegram, kamar yadda Qatar mai shiga tsakani da Amurka suka tabbatar tun farko.
Wallafawa ranar:
Masu shiga tsakani sun yi ta kokarin kulla yarjejeniya don ba da damar sakin kusan fursunoni 240 galibi Isra'ilawa da aka kama a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma tsagaita wuta a Gaza, inda aka kashe fiye da mutane 13,000 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.
Rahotanni sun ce ana kuma tattaunawa kan batun sakin wasu Falasdinawa da suka hada da mata da yara a gidajen yarin Isra'ila, a tattaunawar mai tsanani da Qatar ke shiga tsakani.
Masu shiga tsakani
Firaministan Qatar a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa an kama hanyar cimma yarjejeniyar 'yantar da wasu daga cikin wadanda ake tsare da su.
Shima shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya yi amanna cewa an kusa cimma yarjejeniyar kubutar da wadanda aka kama.
Isra'ila na ci gaba da kai hare-hre
A halin da ake ciki daruruwan Falasdinawa ne suka makale a cikin asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza wanda tankokin Isra'ila suka kewaye, inda WHO ta ce harin da Isra’ila ta kai a baya- bayan nan cikin asibitin ya kashe akalla mutane 12.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu