Isa ga babban shafi

Harin Isra'ila ya kashe kwamandan Hezbollah da wasu mayaka biyu

Cibiyoyin tsaro a Lebanon sun bayyana fargabar fuskantar karin hare-hare a wasu sassan kasar tun bayan da wani harin da Isra’ila ta kai abirnin Nabatiyeh na kasar ya kashe wani babban kwamandan kungiyar Hisbullah da mayaka biyu da kuma fararen hula 7. 

wani harin Isra'ila a Lebanon
wani harin Isra'ila a Lebanon AP - Hussein Malla
Talla

Harin na Isra’ila ya fada kan wani muhimmin ginin ne wanda hakan ya yi sanadin mutuwar wadanda ya rutsa da su tare da jikkata wasu da dama.

Ita dai Hisbullah dake samun goyon bayan Iran ta shiga wata ‘yar tsama ce tsakaninta da dakarun Isra’ila tun bayan da rikici ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata tsakanin Isra’ila da Hamas.

A cikin wannan yanayi ne dai yayin da suka gwabza kazamin fada  Isra’ila ta fitar da wani sakon jawabi dake nuna cewa dakarunta sun kashe Kwamandan Hisbullah Ali AL-Debs da mataimakinsa da kuma wani mayakinsu 1 a birnin Nabatiyeh a ranar laraba da ta gabata.

Wata majiya a Lebanon ta bayyana cewa baya ga kisan kwamandan da Isra’ila tayi tare da wasu ‘yan Hisbullah biyu wannan harin ya rutsa da wasu fararen hula 7 ‘yan gida daya.

Wannan rasa ran ya sa adadin fararen hula ya kai 10 a hare-haren da Isra'ila ta kai ranar Laraba, wanda shi ne mafi yawa da aka kashe tun bayan barkewar rikicin kan iyakar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.