Isa ga babban shafi

Amurka da Tarayyar Turai sun samar da hanyar gaggauta kai kayan agaji Gaza

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta isa kasar Cyprus, domin duba shirye-shiryen aika kayan agaji zuwa Gaza da yaki ya daidaita ta teku.

Kayan agajin Amurka ga 'yan gudun hijira a Gaza.
Kayan agajin Amurka ga 'yan gudun hijira a Gaza. via REUTERS - US Central Command via X
Talla

Wannan dai na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da cewa, sojoji za su kafa tashar jirgin ruwa na wucin gadi daga gabar tekun Bahar Rum na Gaza domin tallafawa kayan da aka kai.

Kokarin Amurka da Turai na kara kaimi wajen kai kayan agaji Gaza a yanzu, ya nuna rashin jin dadinsu kan yadda Isra'ila ke yi a yankin.

Yunkurin kafa hanyar teku domin isar da kayan agaji na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fargabar yaduwar yunwa a tsakanin mutane miliyan 2.3 na Gaza da yaki ya tagayyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.