Isa ga babban shafi

Jirgin yakin Yemen mara matuki ya kashe mata da kananan yara

'Yan tawayen Huthi da majiyoyin gwamnati na zargin juna da hannu a wani harin wani jirgin sama mara matuki a kasar Yemen ya kashe fararen hula biyar a yau Asabar.

Magoya bayan 'Yan Houthi
Magoya bayan 'Yan Houthi AP - Osamah Abdulrahman
Talla

Ma'aikatar lafiya da ke karkashin ikon 'yan tawaye ta ce, an kashe mata uku da yara biyu a lokacin da suka je diban ruwa a rijiya, tana mai zargin dakarun da ke biyayya ga gwamnati da kitsa wannan hari.

Mayakan Houthi
Mayakan Houthi AP - Osamah Abdulrahman

An kai harin ne a lardin Taez, a wani yanki da ke karkashin gwamnati, inda wata  majiyar tsaron yankin da ta bukaci a sakaya sunanta,ta tabbatar da mutuwar fararen hula biyar, ta kuma ce 'yan tawayen ne suka kashe su.

Wani jami’in soji a bangaren gwamnati ya ce, “Sojojin gwamnati ba su da jirage marasa matuka, kuma ba su taba gudanar da irin wannan aikin ba.

Wasu daga cikinyaran Yemen da yaki ya tilastawa canza wurin zama da iyayensu
Wasu daga cikinyaran Yemen da yaki ya tilastawa canza wurin zama da iyayensu ©UNICEF/YPN-Alaa Noman

A shekara ta 2014 ne mayakan Huthi da ke samun goyon bayan Iran suka kwace iko da Sana'a babban birnin kasar Yemen, lamarin da ya sanya Saudiyya shiga tsakani.

Wannan yakin da aka share kusan shekaru tara ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan mutane da kuma tilastawa da dama tserewa daga gidajensu, sannan kuma ya haifar da daya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya.

Mayakan Houthi na Yemen
Mayakan Houthi na Yemen AP - Osamah Abdulrahman

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada a kasar Yemen tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta na watanni shida da aka kulla a watan Afrilun 2022, har ila yau 'yan tawayen Huthi na ci gaba da kai hare-hare na jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya da Tekun Aden da suka ce suna da alaka da Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.