Isa ga babban shafi

Biden ya kira Netanyahu ta waya don duba hanyar kubutar da mutanen da Hamas ke tsare da su

Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho a yau Lahadi, inda ya sake duba tattaunawar da ake yi na kubutar da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin da suka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba,sanarwa daga fadar shugaban Amurka.

Joe Biden Shugaban Amurka .
Joe Biden Shugaban Amurka . AP - Evan Vucci
Talla

Amurka da Isra’ila na nazari da sa ran lallubo hanyoyin sako mutanen da aka yi garkuwa da su tare da tsagaita bude wuta nan take a Gaza, in ji sanarwar fadar White House, yayin da kokarin diflomasiya ke kara kaimi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da aka dade ana nema a yankin da yaki ya daidaita.

Dakarun Isra'ila a yankin Gaza
Dakarun Isra'ila a yankin Gaza via REUTERS - Handout .

Gwamnatin Isra'ila ta fuskanci matsananciyar matsin lamba daga kawayenta na duniya kan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma masu zanga-zanga a cikin Isra'ila da ke neman a sako mutanen da kungiyar Hamas.

Masar da Qatar da kuma Amurka sun shafe watanni suna kokarin shiga tsakani a wata sabuwar sulhu.

Sansanin yan gudun hijira a yankin Gaza
Sansanin yan gudun hijira a yankin Gaza AFP - -

Biden da Netanyahu "sun kuma tattauna batun karuwar isar da agajin jin kai zuwa Gaza ciki har da shirye-shiryen bude sabbin mashigar arewacin kasar daga wannan makon," in ji sanarwar.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu © Leo Correa / Reuters

"Shugaban ya jaddada bukatar ci gaba da dorewar wannan ci gaban da kuma inganta shi cikin cikakken hadin kai da kungiyoyin agaji," in ji ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.