Isa ga babban shafi

Mjalisar dokokin Iraqi ta haramta alaƙar soyayya tsakanin jinsi guda

MajaIisar dokokin Iraqi ta zartar da dokar da ta haramta alaƙar soyayya tsakanin jinsi guda, inda ta yi tanadin hukuncin shekara 10 zuwa 15 a gidan yari ga duk wanda aka kama da karya dokar, a wani mataki da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi Allah wadai da shi.

https___cloudfront-us-east-2.images.arcpublishing.com_reuters_AD3K6W5DK5KH7M5G5PLVMGHQEE
MajaIisar dokokin Iraqi ta zartar da dokar da ta haramta alaƙar soyayya tsakanin jinsi guda, inda ta yi tanadin hukuncin shekara 10 zuwa 15 a gidan yari ga duk wanda aka kama da karya dokar, a wani mataki da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi Allah wadai da shi. © REUTERS
Talla

Gyaran da aka yi wa dokar hana karuwaci na shekarar 1988 wanda ƴan majalisu 170 cikin 329 suka halarta, za’ a yanke wa masu canza jinsi hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari.

Ƙarkashin sabuwar dokar, masu goyon bayan luwaɗi da maɗigo da kuma karuwanci zu su fuskanci hukuncin ɗaurin ƙarancin shekaru 7 a gidan yari, yayin da ƴan daudu ke fuskantar ɗaurin shekara ɗaya zuwa uku.

Kazalika likitocin da ke yin tiyatar sauya jinsi ga masu buƙata, zasu fuskanci hukucin da zai kai shekaru uku a gidan yari.

Ƙafin gyara ga dokar ta 1980 ta yi tanadin hukuncin kisa ne ga masu neman jinsi guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.