Turkiyya da Italiya na neman maye gurbin Faransa a Afirika
Turkiyya da Italiya sun bayyana fara samun matsaya guda a kokarin da suke yi na fadada tasirinsu na tattalin arziki da diflomasiyya a nahiyar Afirka.
Wallafawa ranar:
Kasashen biyu, na neman damar yin hadin gwiwa da kasashen nahiyar a fannin tsaro, makamashi da kuma bakin haure, a daidai lokacin da daddadiyar tasirin Faransa a Africa ke raguwa.
A wannan watan ne majalisar dokokin Somaliya ta amince da wata yarjejeniya da Turkiyya na ba da kariya da taimakon ruwa a fannin gina sojojin ruwan Somaliya, wani mataki ne a yunkurin da Turkiyya ke yi na fadada ayyukanta a Afirka.
Yarjejeniyar ta tsaro ta biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma kan hakar makamashi a Somaliya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu