Isa ga babban shafi

Tawagar Hamas ta shiga tattaunawar tsagaita wuta kan yaƙin Gaza a Masar

Tawagar wakilan Hamas za ta ziyarci birnin Alkahira a yau litinin domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsagaita wuta a Gaza.Wannan dai na zuwa ne yayin da masu shiga tsakani ke kara kaimi wajen cimma matsaya gabanin harin da Isra'ila ke shirin kaiwa a kudancin birnin Rafah.

Abu Ubaida, kakakin kungiyar Izz el-Deen al-Qassam Brigades, yana nuna karimci a lokacin da yake jawabi kan bajekolin makaman Isra'ila. 11 ga Nuwamba, 2019.
Abu Ubaida, kakakin kungiyar Izz el-Deen al-Qassam Brigades, yana nuna karimci a lokacin da yake jawabi kan bajekolin makaman Isra'ila. 11 ga Nuwamba, 2019. © REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Wani jami'in Hamas da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tawagar za ta tattauna kan batun tsagaita wuta da Hamas din ta mika wa masu shiga tsakani na kasashen Qatar da Masar, da kuma martani ga Isra'ila.

Sai dai Jami’in bai bayyana cikakkun bukatun Hamas din na baya-bayan nan ba, amma wata majiya ta yi bayani kan tattaunawar, inda ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ana sa ran Hamas ta mayar da martani kan kudurin tsagaita wuta da Isra'ila ta gabatar a ranar Asabar.

Sakin fursunoni

Majiyar ta ce tattaunawar ta hada da yarjejeniyar amincewa da sakin fursunonin da ta ke rike da su fiye da 40 domin sakin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yari na Isra'ila.

Sai batu na biyu da za’a tattauna shi ne martanin da Isra'ila zata yi kan bukatar sulhu da Hamas ta yi domin tsagaita wuta na dindindin.

Kazalika bayanai sun ce bayan matakin farko, Isra'ila za ta ba da damar zirga-zirga tsakanin kudanci da arewacin Gaza da kuma janye wani bangare na sojojinta daga Yankin.

Tun farko, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce harin da Isra'ila ke shirin kai wa Rafah zai kasance " bala'i mafi muni a tarihin al'ummar Palasdinu" kuma Amurka ce kawai za ta iya takawa ƙasar Yahudawan birki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.