Isa ga babban shafi

Ana dakon martanin Hamas kan bukatar tsagaita wuta a Gaza

Dai dai lokacin da kasashen Amurka da Birtaniya ke mika bukatar ganin Hamas ta aminta da tayin shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki 40 masu zuwa, wani babban jami’in kungiyar ya bayyana cewa yunkurin tsagaita luguden wutar da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa ba wai wani yunkuri ne na tausaya ba, face muradan kasashen dake mara baya ga Isra’ila.

Taron shugabannin kasashen da ke shiga tsakani game da bukatar tsagaita wuta a Gaza
Taron shugabannin kasashen da ke shiga tsakani game da bukatar tsagaita wuta a Gaza REUTERS - Evelyn Hockstein
Talla

Bayan doguwar tattaunawar Hamas da Isra’ila bisa jagorancin kasashen Masar da Qatar ne, sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya mika bukatar ganin Isra’ilan ta amince da tayin don tsagaita yakin na akalla kwanaki 40 da zai bayar da damar musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai babban jami’in Hamas Osama Hamdan ya shaidawa manema labarai cewa ba wai bisa tausayawar cin zarafin fararen hula ko kuma halin da yankin na Gaza ke ciki ne kasashen Amurka ta Birtaniya ke fatan tsagaita wutar ba face kan muradin kansu.

Ko a safiyar yau Talata Isra’ila ta kashe mutane 3 a harin da ta kai sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat baya ga wasu mutane 2 a tsakar birnin Gaza da ke nuna yadda zuwa yanzu ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 34,480.

A dai-dai lokacin da ake ci gaba da dakon martanin Hamas game da batun tsagaita wutar na wucin gadi, wasu bayanai da ke fitowa daga kafar watsa labarai ta CNN na nuni da cewa Hamas din ba ta da isassun Fursunonin da zata yi musaya da su, bare a kai ga cimma yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.