Isa ga babban shafi

Shugaba Petro na Colombia ya sanar da yanke huldar diflomasiya da Isra'ila

A yau Laraba ne ,Shugaban Colombia Gustavo Petro ya sanar da yanke duk wata huldar diflomasiya da Isra'ila, yana mai kiran Firaminista Benjamin Netanyahu a matsayin "mai kisan kiyashi".

Shugaban Colombia Gustavo Petro, a babban birnin kasar Bogota
Shugaban Colombia Gustavo Petro, a babban birnin kasar Bogota AFP - DANIEL MUNOZ
Talla

Shugaban na Colombia na bayyana cewa kama daga gobe Alhamis kasarsa za ta katse duk wata hulda Isra’ila ,shugaban na Colombia bangaren hagu na farko a tarihin kasar da ya dau irin wannan mataki, ya na mai fadar haka ne a wani jawabi ga magoya bayansa a babban birnin kasar Bogota.

Shugaban Colombia Gustavo Petro a jiya Talata ya zargi Isra'ila da aikata "kisan kare dangi" ga Falasdinawa a zirin Gaza, yana mai bayyana "cikakken hadin kai" tare da takwaransa na Brazil Luiz Inacio Lula Da Silva.

SDhugaban Colombia  Gustavo Petro
SDhugaban Colombia Gustavo Petro © AFP - LUIS ROBAYO

Shugaban Brazil cikin fushi y ana mai cewa "a Gaza, an yi kisan kare dangi. Dubban yara da mata da tsoffi ne ake kashewa.

 Shugaban na Colombia na bayyana cikakken goyon bayan ga Shugaban Brazil wanda a makon da ya gabata ya zargi Isra'ila da aikata "kisan kare dangi" ga Falasdinawa a zirin Gaza.

Shugaban Brazil ,Luiz Inácio Lula da Silva
Shugaban Brazil ,Luiz Inácio Lula da Silva AFP - RICARDO STUCKERT

Biyo vayan wannan martani daga Shugaban Colombia,ministan harkokin wajen Isra'ila, Isra'ila Katz, ya ce Lula a halin yanzu ya kasance mutumin da ba shi da wuri a Isra'ila "har sai ya nemi afuwa biyo vayan wadanan  kalamansa."

Sansanin yan gudun hijira a yankin Gaza
Sansanin yan gudun hijira a yankin Gaza AFP - -

Kasashen Brazil da Colombia sun goyi bayan karar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar a gaban kotun duniya ta ICJ a birnin Hague bisa zargin keta yarjejeniyar kisan kare dangi ta shekarar 1948.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.