Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Farfesa Abba Gambo kan matakan da gwamnatoci ke dauka a Najeriya game da noma
Yanzu haka damina ta fara sauka a wasu sassan arewacin Najeriya, yayin da manoma ke shirin tinkarar aikin gona gadan gadan domin magance matsalar karancin abincin da kuma tsadar shi da aka fuskanta. Dangane da shirye shiryen noman, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan aikin noma.16/05/202403:06 -
Attahiru Bafarawa kan shirin ƴan adawa na tinkarar jam'iyya mai mulki a 2027
A Najeriya, yanzu haka wasu daga cikin manyan ‘yan adawar ƙasar cikin su harda wadanda suka tsaya takarar zaɓen shekarar 2023 sun fara tintibar juna domin tsara yadda za su tinkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyya domin kalubalantar gwamnati mai ci.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa. Kuna iya latsa alamar sauto domin sauraren hirar.15/05/202403:18 -
Farfesa Kailani Muhammed a kan batun satar danyen mai a Najeriya
Hukumomin Najeriya sun ce sun kama jiragen ruwa 14 da ake satar danyan man fetur a Neja Delta tsakanin watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan Maris.Rundunar dake aikin samar da tsaro a Jihar Rivers tace wannan bai hada da kananan jirage 90 da kuma mutane 74 da ta kama ba, wadanda ke yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Kelaini Muhammed, masani a kan harkar gas da man fetur, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.14/05/202403:31 -
Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi
Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.09/05/202406:33 -
Malam Issoufou Boubakar Magaji kan kudurin Benin na hana jiragen man Nijar safara
Jamhuriyar Benin ta sanar da cewa ta dakatar da fitar da man da Nijar ke yi har sai ta dube iyakar da ta rufe.08/05/202403:32 -
Dr Abdulhakeem Garba Funtua kan yadda Isra'ila ke shirin yin gaban kanta wajen kai hari Rafah
Kungiyar tarayyar Turai da Amurka sun gargadi Isra'ila a shirin da take yi na kai hari Rafah, duk da cewa alamu sun nuna cewa kasar bata da shirin dakatar da kudurin nata.07/05/202403:26 -
Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi
Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3.06/05/202403:30 -
Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin.03/05/202403:41 -
Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.02/05/202403:06 -
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23 -
Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Nuhu Abbayo Toro na TUC kan ranar ma'aikata a Najeriya
Yau ake bikin ranar ma’aikata ta Duniya, wadda a bana ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarin matsalolin da a wasu sassa ko kasashe za iya cewa ruɓanyawa suka yi, musamman ma ƙalubalen matsin tattalin arziƙi.01/05/202403:23 -
Dr Kasim Kurfi kan yadda darajar nairar Najeriya ke kwan-gaba kwan-baya
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya
Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500 a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.29/04/202403:27 -
Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa
Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya.26/04/202405:17
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.