Isa ga babban shafi

Kotun ɗaukaka ƙara ta samar wa Trump sauƙi a shari'ar rashawa da ake masa

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump  ya samu wata dama a jerin shari’un da ake masa a wannan Litinin, bayan da wata kotun daukaka ƙara ta rage kudin belin da ya kai kusan rabin biliyan na dala da ake bukata daga wajensa, tare da ba shi ƙarin kwanaki 10 ya biya wani sashe na kuɗin.

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump. © Carolyn Kaster / АР
Talla

Ɗan takarar na jam’iyyar Republican ya samu wannan labari mai faranta rai ne a yayin da ya ke gaban wata kotu a birnin New York a kan batun da ya shafi bada toshiyar baki ga wata jarumar fina-finan batsa don ta yi shuru da bakinta a kan wata alaka da ta taɓa haɗa su.

A wannan Litinin ne wa’adin da aka diɓar wa Trump a kan biyan wadannan maƙudan kuɗaɗe gabaninn daukaka ƙarar da yi a game da hukuncin da wata kotu ta yanke cewa zai biya tara sakamakon laifin kara yawan kuɗaɗen da ya  mallaka.

Trump  ya fito ƙarara ya bayyana cewa ya gaza samun wadannnan kudaɗe, kuma hakan zai jefa shi cikin haɗarin rasa wani ɓangare na kadarorinsa.

Hukuncin da kotu ta yanke a wannan Litinin na nufin cewa Trump  yana da ƙarin wa’adin kwanaki 10 da zai biya dala miliyan dari da 75 kawai.

Trump ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumuntarsa na Truth Social app cewa zai yi biyayya da hukuncin kotun daukaka ƙarar.

Trumpmai shekaru 77 ya wayi gari ne da batutuwa biyu a gaban kotu, wanda ɗaya daga cikinsu shine shari’ar da ake masa a kan biyan toshiyar baki ga jarumar fina-finan batsa, Stormy Daniel.

 

Gabanin shiga cikin kotu a Litinin ɗin na, Trump ya shaida wa manema labarai cewa ana masa bita-da-ƙulli ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.