Isa ga babban shafi

Amincewa da haramta TikTok na iya hana Biden sake lashe zaben shugaban Amurka

Bayanai daga Amurka na cewa matukar Shugaban kasar Joe Biden ya amince da rattaba hannu kan dokar haramta amfani da kafar Tik-tok a kasar, hakan zai yi tasiri kwarai wajen bashi matsala a zabe mai zuwa.

Shugaban Amurka, Joe Biden.
Shugaban Amurka, Joe Biden. © Kevin Lamarque / Reuters
Talla

Dambarwar haramtawa Amurkawa amfani da kafar Tiktok din ta samo asali ne tun bayan da kasar ta zargi kamfanin da yi mata liken asiri ko kuma kutse cikin rumbun adana muhimman bayanan ta duk da dai bata bada wata gamsashiyar hujja ba.

Sai dai China, wadda ita ce mai mallakin Tiktok ta ce ikirarin na Amurka bashi da tushe ballantama makama, illa dai hassada ce ta siyasa da kuma yunkurin ganin China bata samar da wani abu karbabbe a duniya ba.

To sai dai ana ganin cewa haramta tiktok din zai shafi takarar Biden ganin cewa watakila ma’abota Tiktok din a Amurka su huce haushi ta hanyar hana shi kuri’a.

Kididdiga ta nuna cewa kaso 60 na masu amfani da kafar sada zumunta ta Tiktok a Amurka magoya bayan jam’iyyar Democrats ne don haka Biden zai yi taka tsantsan waje ganin bai rasa yawan wannan jama’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.