Isa ga babban shafi

EU za ta samar da yuro biliyan 7 ga Masar don kawar da matsalar bakin-haure

Tarayyar Turai ta sanar da samar da yuro biliyan 7 da miliyan dari 4 ga Masar, tare da habaka dangantakarsu, a matsayin wani bangare na matakin taka wa bakin-haure da ke kwarara Turai birki.

Ursula von der Leyen, shugabar hukumar Tarayyar Turai.
Ursula von der Leyen, shugabar hukumar Tarayyar Turai. © Reuters
Talla

Wannan yarjejeniya ta daga dangantakar Tarayyar Turai da Masar zuwa ta cude ni in cude ka, kuma an kaddamar da ita ce a yayin da tawagar jagororin Turai ta ziyarci birnin Alkahira na Masar.

An tsara wannan yarjejeniya ce ta inda za ta inganta hadin kai a bangaren makamashi mara gurbata muhalli, kasuwanci da tsaro, a yayin da za ta bada gudummawa da kuma rance a cikin shekaru 3 masu zuwa ga Masar, waddda ke fama da matsalar tattalin arziki.

A cikin takaitaccen bayanin da tarayyar Turai ta yi a wani rahoto, za a yi amfani da yuro biliyan 5 wajen samar da rance, dala miliyan dari 6 wajen gudummawa, sannan a saka jari da dala biliyan 1 da miliyan dari 8.

Fira ministar Italiya, Giorgia Meloni, wadda ta yi wannan balaguro tare da shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, Fira ministan Girka, Belgium da Austria ta ce yarjeniyoyin hanya ce mai armashi ta dakile kwararar  bakin-haure zuwa Turai.

Gwamnatocin yankin Turai sun damu matuka a game da yanayin da Masar, kasar da ke da yawan al’umma miliyan 106, ke ciki, inda da dama ke yin kaura zuwa Turai duba da matsin tattalin arzikin da ta fada ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.